Yari Ya Raba Shanu 370 Da Raguna 3,500 domin bikin Sallah.
Tsohon gwamnan da ake zargi da almundahana na biliyoyin naira, ya raba Sshanu 370 da raguna 3,500 domin bikin Sallah.
A watan Mayu ne dai wata babbar kotun tarayya ta bayar da umarnin kwace kadarori da wasu kudade na wucin gadi na Yari, tsohon gwamnan Zamfara.
Tsohon gwamnan jihar Zamfarar Abdulaziz Yari da ake zargi da satar biliyoyin Naira na dukiyar al’umma, ya sayo shanu 370 domin rabawa shugabannin jam’iyyar APC da marasa galihu don yankawa ga Sallah.
Shugaban kwamitin rabon kayayyakin kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na jihar, Lawal Liman ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da kason shanun ga wadanda zasu amfana a Gusau ranar Asabar.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa a farkon makon nan ne tsohon gwamnan ya raba raguna 3,593 a fadin jihar domin bikin daya.
Liman ya ce an yi hakan ne da nufin taimakawa marasa galihu wajen gudanar da bukukuwan Sallah cikin sauki.
Ya ce wadanda suka ci gajiyar shirin sun kuma hada da sabbi da tsofaffin shugabannin jam’iyyar APC daga mazabu 147 da shugabannin kananan hukumomin jam’iyyar.
Liman ya ce, “Sauran wadanda suka ci gajiyar tallafin sun hada da malaman addinin Islama, kungiyoyin matasa da mata na APC, kungiyoyi da kuma shugabannin al’umma a jihar”.
Ya kuma yabawa tsohon gwamnan bisa goyon bayan al’ummar jihar.
Liman ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da lokacin bikin babbar Sallah wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da ma Najeriya baki daya.
Majiyar Popular News Hausa ta PremiumTimes ta ruwaito yadda hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kama Yari tare da tsare shi, inda take binciken zargin almubazzaranci na biliyoyin naira a lokacin da yake gwamnan Zamfara tsakanin shekarar 2011-2019.
Ana kuma binciken Yari bisa zargin cin gajiyar Naira biliyan 80 da ake zargin tsohon akawun gwamnatin tarayya Ahmed Idris ya sace.
A watan Mayu, babbar kotun tarayya ta ba da umarnin a kwace kadarori da wasu kudade na wucin gadi da aka samu a hannun Yari.
Duk da binciken cin hanci da rashawa dai, Yari ya fito a matsayin dan takarar sanata a jam’iyyar APC a Zamfara a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.
