November 19, 2026

Yanzu Yanzu: Mataimakin Kakakin Majalisar Bauchi Ya Sha Kaye A Zaɓen Fidda Gwani

0

Daga Khalid Idris Doya

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin jihar Bauchi, Honorable Ɗanlami Ahmed Kawule ya sha ƙasa a zaɓen fitar da gwani na ɗan Majalisar tarayya mai neman wakiltar mazaɓar ƙaramar hukumar Bauchi a ƙarƙashin jam’iyyar PDP da ke mulki a jihar.

Wakilinmu ya labarto mana cewa Alhaji Aminu Ali Garu shine ya kada Kawule da gagarumar nasara bayan fafata zaɓen da aka gudanar ta hanyar amfani da wakilai wato (delegates) a yau Lahadi a Bauchi.

Da ya ke bayyana farin cikinsa bisa wannan nasarar, Aminu Garu ya gode wa Allah bisa samun nasara da ya yi, ya kuma gode wa delegates bisa amincewa masa da zabinsa.

Ya kuma yi kira ga waɗanda suka fafata neman kujerar tare da su wato sauran mutum biyun da suka faɗi da su haɗa hannu wajen samun nasarar jam’iyyar a babban zaɓen 2023 da ke tafe.

Duk ƙoƙarin da ‘yan jarida suka yi don jin ta bakin Kawule bisa wannan shan kayen da ya yi abun ya citura zuwa yanzu.

Wakilinmu ya nakalto cewa, shi dai mataimakin Kakakin Majalisar yanzu haka shine ke wakiltar mazaɓar Zungur, Galambi da Miri a Majalisar dokokii ta jihar, wanda tunin kuma jam’iyyar ta zabi wani a kan wannan kujerar da zai daga mata tutarta na neman wannan mazabar a zaben 2023.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *