September 18, 2026

YANZU-YANZU: Kotu ta yanke wa jarumar Kannywood Sa’adiya Haruna hukuncin wata 6 a gidan yari

0

Kotun Majistire, da ke zaman ta a Filin Jirgin sama na Kano, ta yanke wa wata jarumar Kannywood kuma shahararriyar mai amfani da kafar sadarwa ta instagram, Sadiya Haruna hukuncin ɗaurin watanni shida.

Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Muntari Dandago, ta yanke hukuncin ne ba tare da zaɓin tara ba.

An yanke wa Sadiya wannan hukuncin ne bisa kalaman ɓatanci da ta yi ga wani ɗan wasan kwaikwayo na Kannywood, Isah I. Isah a shafinta na Instagram.

Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa tun a ranar 16 ga watan Oktoba, 2019 a ka fara gurfanar da Sadiya a kotun.

Daily Nigerian Hausa

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *