Yan Sanda Sun Kama Masu Yankan Aljihu A Jigawa.
Rundunar yan sandan Najeriya ta samu nasarar kama wasu mutane 6 da ake zargi da cewa yan-sane ne a karamar hukumar Hadejia dake cikin Jihar Jigawa.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan Najeriyar a jihar Jigawan DSP Lawal Shi’isu ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Dutse.
Ya bayyana cewa mutanen masu shekaru tsakanin 18 zuwa 25, an kama su ne bayan da suka zare ma wani mutum mai suna Ibrahim Garba naira ₦13,000 da wayar salula a kasuwar Baturiya.
Kazalika mai magana da yawun rundunar yan sandan ya ce rundunar ta kama wasu mutane 6 da kwayar Diazapom 180 da ake zargin dilolin kwaya ne a duk a cikin karamar hukumar ta Hadejia, Popular News Hausa.
Ya ce an kama su ne a lokacin da jami’an yan sanda hadin gwiwa da yan vigilante suka kai samame a wasu wuraren da ake aikata laifuka dake Janbulo da kasuwa Buturiya.
Mai magana da yawun rundunar ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba wurin yin sintiri, tare da kai samame a maboyar masu aikata laifuka.
Daga nan sai ya ce za a mika wadanda ake zargin gaban kuliya da zarar an kammala bincike.
