September 18, 2026

‘Yan Sanda Sun Kubutar Da Mutane 8 Da AKa yi Garkuwa Da Su, Sannan Sun Kashe Mutum Daya Da Kwato Dabbobi 82 A Katsina.

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta yi nasarar kubutar da mata biyar da ‘ya ‘yan su uku daga hannu masu garkuwa da jama’a domin neman kudin fansa.

Kakakin rundunar a Katsina SP Gambo Isah ya bayyana haka ga manema labarai a lokacin da yake nunawa ‘yan jarida mutanen da aka bukutar da gawar dan bindiga guda da suka kashe.

SP Gambo Isah ya ce jami’ansu na ƙaramar hukumar Malumfashi sun sami kira cewa ga ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun kawo hari a garin Fuloti da Karfi na ƙaramar hukumar Malumfashi har sun dauki mata da sace dabbobi kuma sun bi ta Ƙanƙara.

Ya ce da jin haka sai baturan ‘yan sanda na ƙaramar hukumar Kankara ya haɗa wata tawaga ta musamman inda suka tare ‘yan bindiga akan hanyarsu ta kusa da Zurunkutun a tsakanin Kankara da Shene.

“A wannan yanayi jami’an mu sun nasarar tarwatsa yan bindigar tare da kashe mutum daya har lahira, wanann mun kubutar da mutane hudu da ya yan su da bindiga kirar AK 47 da kuma shanu guda tamanin da takwas.” Inji shi.

SP Gambo Isah ya ce a wani labarin mai kama da na farko, rundunar ‘yan sandan ta samu rahotan cewa ‘yan bindiga sun tare hanyar Kankara Zango suna cin mutuncin jama’a ba gaira ba da dalili

Haka kuma wannan tawaga ta yi nasarar tarwatsa yan ta’addan ta hanyar bude masu wuta kan mai uwa da wabi.

Ya ce daga cikin yan ta’addan daya ya rasa ransa a lokacin artabu sannan sun sami nasarar kama mashi din hawa kirar Boxer wanda baya da lamba kuma na dan bindigar ne.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *