September 17, 2026

Yan Sanda Sun Kama Yan Vigilante 6 A Kano Bisa Zargin Su Da Kashe Wani Malamin Makarantar Allo.

0

Kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta BBC Hausa ta bayyana, yan vigilante na aikin sintiri cikin dare, sai suka ci karo da malam Musa Lawal dauke da jariri.

Hakan ya sanya yan vigilante suka zargi malamin da cewa sato jaririn yayi.

Saidai marigayin ya bayyana masu cewa, cikin tahwasa ya tsinci jaririn. Amma wannan hujjar bata gamsar da su ba, saida suka tafi da shi caji ofis din.

Nan ne ake zargin sun ta bugun shi har ya ce ga garin ku nan.

Wani dan uwan mamacin malam Muhammad Salihu da aka yi fira da shi ya bayyana cewa, “tun kafin ya sauka daga saman mashin, wani ya zo yana fada masa cewa ya zo ya ga malam Musa cikin wani mawuyacin hali a ofishin yan vigilante na Gidan Kankare dake Kano.”

Ya ce, ” da suka isa ofishin yan vigilante tare da wakilin mai unguwa, sai suka ki buɗe masu don ganin halin da yake ciki sai da suka kai ruwa rana.”

Rundunar yan sandan jihar Kano ta bakin mai magana da yawunta SP Haruna Kiyawa ta tabbatar da kama yan vigilante 6.

Kuma ta ce hakan nada nufin gano gaskiyar labari dangane da kinsan da ake zargin sun yi ma malam Musa Lawal.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *