Yan Sanda Sun Kama Yan Ta’adda Daban Daban A Zamfara.
Rundunar yan sanda jihar Zamfara ya gabatar da mutane 10 da ake zargi da aikata laifukan da suka haɗa da yin ta’addanci, taimaka ma yan ta’addan da kuma yin sojan gona.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar SP Muhammad Shehu ya ce mutanen na cikin wadanda ake zargi da addabar al’ummomin kananan hukumomin Gusau, Kauran Namoda, Tsafe da kuma karamar hukumar Bangudu.
Ya ce ɗaya daga cikin mutanen ya bada labari da bakinshi cewa, ya na cikin yan ta’addan da ke addabar Mada da Kotar Koshi, kuma ya na da bindiga kirar AK47 ɗaya da kuma harsasai guda 174.
Hakanan kuma, akwai wani mai suna Zubairu da ya fito daga karamar hukumar Tsafe wanda ake tsare da shi, ya ce shi tsohon soja ne, an same shi da bindiga kirar gida, kakin sojoji da ID card na bogi.
