Yan Sanda Sun Cafke Ma’aikacin Bankin da ya Haɗa da Abokin sa suka Sace Miliyan 18 a Katsina
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta yi nasarar cafke wani mutum mai suna Adewumi Bolaji Gabriel ɗan shekaru 28 da ke ƙaramar hukumar Daura bisa zargin haɗa baki da abokinsa inda suka sace kuɗi naira miliyan 18
Hakan ya biyo bayan korafin da mataimakin manajan bankin Access da ke Daura, Okajie-Hubert Erayomo ya shigar inda yake zargin mai kula da sashin katin cire kuɗi ATM Adewumi Bolaji Gabriel da tafka wannan ta’asa.
Bayanin haka yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar kuma ya rabawa menema labarai a Katsina
Kakakin rundunar ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya haɗa kai da wani abokin sa mai suna David Mesioye wanda yake ma’aikaci ne a bankin Access da ke Kafur wanda yanzu ake nema ruwa a jallo inda suka sace naira miliyan 18 da dubu 160 daga asusun ajiyar wani abokin hulɗar bankin Access
Sanarwa ta ƙara da cewa jami’in da ke kula da sashin katin cire kuɗi ATM shine kanwa uwar gami wajen sace waɗannan kuɗaɗai, inda ya yi amfani da kwarewar sa ta aiki a bankin wanda aka gano haka bayan gudanar da binciken kwakwaf.
ASP Abubakar Sadiq ya ƙara da cewa a lokacin gudanar da bincike wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zargin sa da aikatawa, bayan bayyanar shaidun aka gano bayan gudanar da binciken.
A cewar sanarwar, an samu kuɗi naira miliyan 10, 180,000,00 a mabanbantan asusun ajiyar wanda ake zargi sai kuɗi tsaba naira ₦366,900.00 tare da wasu kayayyaki.
Hukumar ‘yan sanda ta ce wanda ake zargi za a miƙa shi gaban kuliya manta sabo da zaran an kammala bincike domin fuskantar shari’a akan laifin da ake tuhumar sa da aikatawa.
