September 18, 2026

‘Yan Bindiga Sun Yi Wa AIG Na ‘Yan Sanda Kwanton Bauna, Tare Da Kashe Dogarin Shi.

0

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba a dajin Lame/Burra dake cikin jihar Bauchi sun kai hari kan ayarin motocin Mataimakin babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya mai kula da shiyya ta 12 AIG Audu Madaki, inda suka raunata shi tare da kashe daya daga cikin jami’an tsaronsa a ranar Talata

Rahotanni sun bayyana cewa, tawagar Madaki dake kan hanyar ta ta fitowa daga Bauchi ‘yan ta’addan sun kai mata hari ne a unguwar Barde Zangidi dake cikin karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi da misalin karfe 2:30 na rana, inji majiyar jaridar Popular News Hausa ta Vanguard.

An bayyana cewa an harbe Madaki tare da jikkata, sannan suka harbe dogarin shi har lahira.

An an bayyana cewa mataimakin babban sufeton yan sandan yanzu haka yana karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba a Abuja, yayin da kuma aka tsaurara matakan tsaro a shiyyar kamar yadda wata majiya ta bayyana.

Majiyar ta ce an tura jami’an ‘yan sanda dauke da makamai zuwa yankin domin kakkabe ‘yan ta’addan.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *