‘Yan Bindiga Sun Kona Sakatariya da Kotun Majistare A Anambra.
Wasu mahara sun kona sakatariyar karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra.
Haka kuma sun kona wata kotun Majistare da ke harabar sakatariyar karamar hukumar.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Ikenga Tochukwu, ya shaida wa LEADERSHIP cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar yau Litinin.
Sai dai ya bayyana cewa ba a samu asarar rai ba a hare-haren biyu.
Tochukwu yayin da yake mayar da martani ga binciken LEADERSHIP game da lamarin ya bayyana cewa: “An dauki matakin gaggawar shiga tsakani na rundunar ‘yan sanda domin dakile barnar da barayin suka yi a sakatariyar karamar hukumar.
Saidai abun takaici, wasu ofisoshi da motocin jami’an da ke cikin karamar hukumar sun kone.
“A halin da ake ciki ba a rasa rai ba kuma an dawo da zaman lafiya a yankin.”
