September 17, 2026

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Makaranta, Sun Kashe Mutum daya, Tare Da Yin Awon Gaba Da 2 Ciki Hadda Rector A Kaduna.

0

Rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da kashe mutum daya da kuma yin garkuwa da shugaban makarantar kididdiga ta gwamnatin tarayya dake Manchok a karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna. Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce an kai harin ne da misalin karfe 8 na daren ranar Litinin lokacin da maharan suka afkawa kauyen, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar AIT.

Ya koka da yadda ‘yan ta’addan suka afka wa al’ummar cikin dare,inda suka kashe mutum daya, yayin da aka yi garkuwa da wata mace ciki har da shugaban karamar hukuma. Harin dai ya zo ne makonni uku da bindige wasu ma’aikatan wucin gadi biyu dake rabon gidajen sauro a hanyar Zangang zuwa Zankan a cikin karamar hukumar.

Majiyar ta ce ‘yan ta’addan sun afka wa al’umma da manyan makamai, inda suka yi ta harbe-harbe, kafin su yi awon gaba da mutanen biyu. Ya kuma koka da yadda wasu al’ummomi a kananan hukumomin ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda kuma jami’an tsaro ba su yi komai ba wajen magance lamarin.

Ya yi kira ga gwamnati da ta karfafa tsaro a yankin, domin dakile ayyukan masu aikata laifuka. Ya kara da cewa har yanzu masu garkuwa da mutanen ba su nemi mahukuntan makarantar ba ko kuma dangin wadanda aka sace.

Saidai har ya zuwa lokacin haɗa wannan rohoton, ba a samu kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna DSP Mohammed Jalige ba.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *