‘Yan Bindiga Sun Cinna Ma Hedikwatar Ƙaramar Hukuma A Ebonyi Wuta.
Rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi ta tabbatar da harin da wasu ‘yan bindiga da ba a tantance ba suka kai a wani sashe na karamar hukumar Ezza ta Arewa.
Majiyar jaridar Popular News Hausa ta jaridar Vanguard ta ce, ‘Yan ta’addan sun bankawa wurin wuta a wanna Litinin ɗin, tare da lalata wasu kayayyaki masu daraja na miliyoyin Naira.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar SP Chris Anyanwu, ya shaidawa manema labarai a Abakaliki cewa, rundunar ta tabbatar da faruwar lamarin.
Anyanwu ya ce: Muna sane da harin, amma har yanzu ba mu samu cikakken bayani ba.
“A yanzu haka, ana ci gaba da bincike don samun cikakken bayani, amma ba a kama kowa ba.”
Da yake bayyanawa manema labarai faruwar lamarin a ofishinsa, shugaban karamar hukumar, Mr. Ogodo Nomeh, ya ce harin ya faru ne da sanyin safiyar wannan Litinin din.
Nomeh ya ce: “ An yi artabu da yan ta’addan da jami’an tsaro a wurin.”
“Wasu daga cikin ‘yan bindigar sun samu raunuka na harbin bindiga.”
“Ya zuwa yanzu ba a kama kowa ba, saboda lamarin ya faru cikin dare.”
“An ta ɓarin wuta kuma da yawa daga cikin ‘yan bindigar sun jikkata.”
“Yanzu muna bi asibiti bayan asibiti don duba mutanen da aka samu da harbin bindiga.”
“Ba mu zargin kowa a yanzu har sai mun kama wadanda ake zargin.”
“Yanzu haka muna tattaunawa da jami’an tsaro da suka yi karo da ‘yan bindigar,” in ji shi.
