September 18, 2026

Yadda Shugaban Shirin Bunkasa Rayuwar Al’umma Ya jagoranci Raba Takin Zamani A Garin Banye

1778069045460

 

Shugaban shirin bunƙasa rayuwar al’umma wato CDP Ferfesa Kamaluddeen Kabir ya jagoranci raban takin zamani na wannan shekarar a garin Banye da ke cikin ƙaramar hukumar Charanci ta jihar Katsin.

 

Rahotanni na nuni da cewa ƙaramar hukumar Charanci ta cire tura wajen haɗa kuɗaɗen takin noman daminar bana wanda gwamna Raɗɗa ya kaddamar a garin Malumfashi.

 

Haka kuma shugaban shirin bunƙasa rayuwar al’umma Ferfesa Kamaluddeen Kabir ya jagoranci hannata wannan taki na zamani ga manoman da suka biya kudaden su.

 

Idan za a iya tunawa a can baya an ta bada sanarwar a biya, kuɗaɗen da wuri wanda yanzu haka gwamnatin jihar Katsina na cigaba da gargadin cewa kadda a sayar da takin fiye da N25, 000 kowane buhu.

 

Sannan gwamnatin jihar Katsina ce ta ɗauki nauyin kai takin duk wararen da za a raba shi ga wadanda suka biya kudaden su baƙi ɗaya.

 

Ferfesa Kamaluddeen ya ce babban laifi wani ko wasu su ƙara kuɗin takin fiye da kudaden da gwamnati ta kayyade farashin takin zamani na kowane buhu.

 

Ya ƙara da cewa duk inda suka tarar an kara kuɗin takin fiye da farashin da gwamnati, to za a mayar da wannan taki sannan za a matakin shari’a.

 

Ferfesa Kamaluddeen ya ƙara jan kunne da cewa akwai jami’an hukumar amsar ƙorafe-ƙorafen al’umma da kuma yaƙi da cin hanci za su yi aikin su idan aka samu rahoton rashin gaskiya

 

Daga ƙarshe gwamnatin jihar Katsina ta ware naira dubu ɗari ga kowace mazaɓa domin daukar dawainiya da kuma buhu 5 na taki ga ‘yan kwamiti

About The Author