Yadda Aka Gudanar Da jana’iza Dada Mahaifiyar Tsohon shugaban Ƙasa Umaru Musa Yar’adua a Katsina
Yadda Aka Gudanar Da jana’iza Dada Mahaifiyar Tsohon shugaban Ƙasa Umaru Musa Yar’adua a Katsina
Mataimakin shugaban ƙasa Sanata Kashin Shettima ne ya wakilci shugaba Bola Ahmad Tunibu a wajen jana’izar Hajiya Dada wanda aka gudanar a tsohon filin wasa da ke cikin garin Katsina.
An fara sallar da misalin karfe 1:55:00 na ranar talata a cikin tsohon filin wasa da ke cikin garin Katsina ana tsaka da ruwan sama.

An rufe marigayiyar ne a makarantar Ɗanmarna cikin birnin Katsina inda daman da ake rufe manyan mutane da da suka haɗa da ‘yan siyasa da masu kuɗi da sarakuna da sauran su
Jim kaɗan bayan kammala sallar Sanata Kashin Shettima ya bayyanawa manema labarai cewa an yi rashin uwa a Nijeriya wanda ya bayyana a matsayin wani gebi da za a daɗe ba a cike shi ba .
Mataimakin shugaban ƙasa ya ƙara da cewa babu abinda marigayiyar take buƙata yanzu kamar addu’a saboda haka ne ya yi addu’ar Allah ya jikanta da rahama.

Bayan kammala sallar jana’izar wanda Sheikh Aminu Yammawa ya jagoranta Sanata Kashin Shettima ya kai ziyarar ta’aziya gidan marigayi Dada a gidan Matawalle Musa Yar’adua da ke cikin birnin Katsina.
Sanata Kashin Shettima tare da manyan ‘yan siyasa da masu rike da muƙaman gwamnati a matakin ƙasa da kuma jahohi ne suka halarci sallar jana’izar.
Manyan mutanen da suka halarci wannan jana’iza ta marigayi Dada sun hada da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyar LP a zaɓen 2023 Peter Obi da mataimakin sa Ahmad Datti.
Sauran sun haɗa da hamshakin ɗan kasuwa wanda kuma ɗan uwar marigayiya ne, Alhaji Ɗahiru Bara’u Mangal da gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa da mataimakin sa Malam Faruƙ Lawal Jobe.
Tare da Mataimakin shugaban majalisar Dattawan Nijeriya Sanata Barau Jibrin Maliya da Sanata Danjuma Goje da Sanata Adamu Aliero da Sarakunan Katsina da Daura.da Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar da ministan gidaje da raya birane Ahmad Musa Dangiwa da tsohon shugaban majalisar dattawan Sanata Ahmad Lawal da tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina Malam Mustapha Inuwa
Da yake amsa tambayoyin ‘yan jaridu mataimakin shugaban majalisar Dattawan Nijeriya Sanata Barau Jibrin Maliya ya bayyana rashin a matsayin wani baban rashi wanda ya shafi duk al’ummar musulmi.
Mataimakin shugaban majalisar dattawan Sanata Barau Jibrin ya ƙara da cewa za a daɗe ana tunawa da marigayi Dada saboda da irin gudunmawa da taimakon musulmi da musulunci wanda ya ce Marigayi ta sadaukar da lokacin wajen yi wa addini da al’umma hidima.

Sanata Barau Jibrin wanda ya jagoranci saura Sanatoci domin kai ziyarar ta’aziya ga abokin aikin su, kuma ɗa ga marigayi Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua shugaban kwamitin sojoji ya yi addu’ar Allah ta’ala ya jikanta da gafara ya kyautata makwancin ta yasa aljanna Firdausi ce makomar ta.
Mataimakin shugaban majalisar ya yi jan hankali ga ɗan marigayiyar Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua da sauran waɗanda ta bari da su yi koyi da ita wajen yi wa al’umma da addini hidima
Sanatoci da suka rufa mas baya sun haɗa da Sanata Abdul Hamid Malam-Madori shugaban kwamitin ‘yan sanda da Sanata Muntari Ɗandutse shugaban kwamitin hukumar bunƙasa ilimin manyan makarantu (TETFUND) da Sanata Aminu Iya Abbas shugaban kwamitin ma’aikatar kimiyya da fasaha ta Nijeriya

Yanzu haka ‘yan uwa da abokan arziki na cigaba da kai ziyarar ta’aziya ga iyalai magariyar a gidan ta da ke Yar’adua cikin birnin Katsina
