September 16, 2026

Tsaro: Majalisar Dokokin Katsina Zata Yi Kwallin Kura Da Buhari Da Masari

0

Majalisar Dokokin jihar Katsina ta yanke hukuncin tunkarar shugaban ƙasa Muhammad Buhari da gwamna Aminu Bello Masari saboda yadda matsalar tsaro ta ƙara ƙamari musamman cikin garin Katsina da kewaye.

Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar Hon. Ali Abu Albarka ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Katsina

Ya ce majalisar dokokin jihar Katsina ta kaɗu ainun da yadda matsalar tsaro ta zama abinda ya zama a wannan lokaci.

“Kullum sai mun amshi Rahotan kai hare-haren wuce gona da iri da ‘yan bindiga ke kaiwa jama’a babu gaira babu dalili” inji shi

Ɗan majalisar ya ce yanayin da tsaro ya shiga a jihar Katsina abin ya ta’azara kuma ba abu ne wanda za a amince da shi ba, dole a dauki mataki domin kawo karshen wannan bala’in da ya adabi jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya

Daga karshe ya ce yana goyon baya matakin da gwamna Aminu Bello Masari ya ɗauka na kiran jama’a su kare kan su daga duk wata barazana.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *