September 18, 2026

Tsananin Rashin Tsaro: Gamayyar Kungiyoyin Farar hula Sun Yi Kiran Addu’o’i Na Musamman A Jihar Katsina

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Gamayyar kungiyoyin farar hula a jihar Katsina sun kaɗu matuƙa saboda ƙaruwar hare haren ‘yan bindiga a wasu garuruwa da ke nuna halin ko in kula da gwamnatin ke yi wa harkar tsaro. Wanda har yanzu ta ƙasa kawo karshen kisan da ake yi wa waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba.

Bayanan hakan yana kunshe ne acikin wata sanarwa da shugaban gamayyar kungiyoyin farar hula a jihar Katsina. Abdulrahaman Abdullahi Dutsima ya sanyawa hannu ya rabawa manema labarai a Katsina.

Sanarwar ta ce ayyukan ‘yan ta’ada sun kai wani matsayi da kullum sai an kai harin wuce gona da iri, saboda yadda ‘yan bindigar ke
sayan makaman kare dangi da kuɗaɗen da ake biya bayan su, bayan sun ɗauke jama’a, sannan hakan na ƙara masu ƙarfi ta yadda suke kara faɗaɗa kai hare haren ba ji ba gani.

“Jihar Katsina a yau ta koma wani wuri na rashin tabbas a rayuwa babu waje ɓoya kuma babu wanda ya tsira, hatta kokuwar
Katsina tana fuskantar barazana, inda sha’anin samar da tsaron dukiya da rayukan al’umma ya zama abu na farko da shuwagabanni ya kamata su yi kafin wani abu, amma abin takaici babu wata hubbasa daga ɓangaren gwamnati na tunkarar wannan matsala inda har takai kuloluwa kasawar hukumomi a wannan sha’ani na tsaro

Haka kuma sanarwa ta ƙara da cewa yanzu babu abinda ya rage sai a koma ga Allah ta hanyar yin addu’o’in neman gafarar Allah tunda duk kira da jan hankali da rubuce-rubucen an riga anyi domin jan hankalin gwamanti akan matsalar tsaro amma shiru kake ji kamar an aiki bawa garin su, zaɓin da rage shi ne addu’o’i

Abdulrahaman Abdullahi ya ce a matsayin su ‘yan Adam mun san cewa mulki na Allah ne kuma shi kaɗai ne zai yi maganin wannan matsala fiye da tunaninms, a daidai wannan gaba gamayyar kungiyoyin farar hula ke kira ga al’umma da su dukufa wajan yin addu’o’i domin Allah ya kawo ɗauki akan wannan al’amari.

Ya ce za a cigaba da yin waɗannan addu’o’i ne a masallatai da kuma mujami’u da makarantun islamiyya da na allo a duk fadin jihar Katsina.

Haka kuma sanarwa ta ce dole al’umma ta ƙara gyara tsakanin ta da Allah mahalicci, a matsayin su na bayin Allah. Haka kuma ya zama wajibi rokon gafarar Allah Ta’ala, sannan a cigaba da tallafawa marasa karfi domin neman yardar Allah ya amshi addu’o’in da za a gudanar na neman zaman lafiya a cikin al’umma.

Daga karshe gamayyar kungiyoyin farar hula a jihar Katsina na miƙa sakon ta’aziyarsu da jaje ga ‘yan uwan waɗanda suka rasa ransa a sakamakon ayyukan ‘yan bindiga. Tare da yin addu’ar Allah ya kawo ƙarshen wannan mummunan yanayi da al’umma ta tsinci kanta aciki, ya maido mata da zaman lafiya a jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *