Tsaffin Sakatarorin Ilimin Rimi A Katsina Sun Bukaci Iyaye Su Taimaka Ma Ilimin Ƴaƴansu.
Tsaffin sakatarorin ilimin karamar hukumar Rimi 2 sun bukaci iyaye su taimaka ma ilimin ƴaƴansu.
Hassan Abdulkadir da Dr. Sirajo Dalhat suka fadi hakan a lokacin bikin bankwana ga tsohon shugaban makarantar al’umma mai suna Community Day Secondary School Majen Gobir, Mujjitaba Abba bayan da ya kwashe shekaru 35 yana aiki.
Kamar yadda ya bayyana, ilimi shi ne muhimmin abu da iyaye za su iya gadarma ƴaƴansu, ba wai dukiya ba.
Hakanan kuma, Dr. Hide Umar Sale ya yi bayani akan mahimmancin taimaka ma kokarin gwamnati a bangaren ilimi domin cimma abinda akan sanya gaba.
Wakilin shugaban karamar hukumar Rimi, Salahuddin Barau ya bada gudunmawa ga shugaban makarantar mai barin gado bisa sadaukarwarshi ga ci gaban ilimin yankin.
