September 18, 2026

Tiyata: An sallami Osinbajo Daga Asibitin Lagos

0

An sallami mataimakin shugaban Najeriya daga asibiti bayan yi mashi tiyata, kamar yadda Dr. Nicholas Audifferen, babban likitan mataimakin shugaban kasar ya ce.

Mai magana da yawun Farfesa Yemi Osinbajo, Laolu Akande ne ya bayyana wa manema labarai hakan yau Litinin a Abuja, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Vanguard.

Ya ce, “an kwantar da mataimakin shugaban kasar a asibitin kasa da kasa taa Duchess dake Lagos, a ranar 16 ga Yuli, saboda karayar da ya samu.”

Ya bayyana cewa “an yi masa tiyatar ba tare da wata matsala ba.”

Ya ce “An kwantar da shi na tsawon kwanaki bakwai, inda aka yi masa aiki.”

Audifferen ya ce an sallame shi kuma yanzu haka yana samun sauki.

Ya ce “Osinbajo na godiya ga daukacin ma’aikatan asibitin karkashin jagorancin babban jami’in gudanarwa, Dr. Tokunbo Shitta-Bey da Daraktan Likitoci, Dr. Adedoyin Dosunmu-Ogunbi bisa kwarewa da ingancin kulawar da su kai mashi.”

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *