September 17, 2026

Tawagar Gasar Mahawara Ta Jihar Katsina Ta Ci Maki 1,553.

0

Tawagar gasar mahawara ta jihar Katsina ta doke ta kwalejin gwamnatin tarayya da ke Daura.

An bada rohotan cewa, tawagar jihar Katsina ta samu nasarar cin maki 1,553, yayinda kwalejin gwamnatin tarayya ta ci maki 1,380.

Taken mahawarar shi ne ” Ya Kamata Rasha Ta Samu Nasara Kan Ukraine Don Amfanin Tsaronta”.

Da yake magana a wurin, shugaban hukumar bada ilimin bai daya ta jihar Katsina Lawal Buhari Daura ya ce manufar shirya mahawarar shi ne, daliban su shirya ma babbar mahawara ta kasa da kasa da za ai a kasar Malaysia.

Ya ce jihar Katsina ita ce za ta wakilci Najeriya, kuma za su bar kasar a ranar 26 ga wannan watan domin zuwa kasar Malaysia.

Ya hori wadanda suka halarci gasar da su linka kokarinsu, tare da zama jakadu na gari ga jihar Katsina dama Najeriya baki daya.

Tunda farko, saida faransifal din kwalejin gwamnatin tarayya da ke Daura Tukur Umar Koko ya bayyana cewa, hukumar SUBEB ce ta shirya gasar mahawarar.

Ya shawarci wadanda aka dama da su a cikin gasar da su linka kwazonsu, tare da zama masu jajircewa.

Babban alkalin mahawarar Yusha’u Maikano ya bayyana daya daga cikin mahalarta gasar mahawarar ta jiha Abubakar Adamu da ke makarantar GDJSS Magama a matsayin wanda ya fi kowane kokari, da kuma lashe maki mafi yawa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *