Taron Jin Ra’ayi: Yadda Mutanen Bagiwa Suka Fito Domin Bayyana Abubuwan Da suke buƙatar Gwamnati Ta yi Masu.
Taron Jin Ra’ayi: Yadda Mutanen Bagiwa Suka Fito Domin Bayyana Abubuwan Da suke buƙatar Gwamnati Ta yi Masu.
Mazaɓar Bagiwa ɗaya ce daga cikin mazaɓo goma sha ɗaya da ke akwai ƙaramar hukumar Mani kuma sun bi sahun saura wajen shiga a dama da su akan batun kasafin kudin 2026 da za a gabatar.

Batun baiwa jama’a dama su miƙa bukatun su domin sanyawa a kasafin kuɗi wani sabon shiri ne da gwamnatin Malam Dikko Umar Raɗɗa ta zo da shi domin yin gwamnati da hannun kowa a cikin.
Shirin baiwa kowa dama su faɗa bukatun su a mazaɓo 361 na fadin jihar Katsina ta zo da sabon salon mulki irin na dimokuraɗiyya wanda kowa zai san cewa ana yin gwamnati da shi.
A tattaunawar sa da manema labarai shugaban ƙaramar hukumar Mani Dakta Yunusa Bagiwa ya bayyana irin yadda al’ummar mazaɓar sa suka fito suka bayya buƙatun su da kansa ba tare da wani haufi ba.

Dakta Yunusa Bagiwa ya nuna jin dadin sa akan yadda jama’a suka fito a wannan mazaɓa da kowa sauran mazaɓo guda goma a ƙaramar hukumar Mani.
A cewar sa sauran mazaɓo an tattauna da bada shawarwari domin cigaban waɗannan mazaɓo.
Ya ƙara da cewa babbar manufar wannan taro shine wannan gwamnati ce ta dimokuraɗiyya wanda kuma take baiwa jama’a dama su tofa albarkacin bakinsu game da abubuwan da suka shafe su na rayuwar Yau da kullum.

” Idan a duba a baya, za a ga cewa kila akwai abinda gwamnati take hange, to amma a wannan karon sai aka baiwa jama’a dama su bayyana abubuwan da suke buƙata gwamnati ta yi masu’ inji shi
Dakta Yunusa ya cigaba da cewa za su tattara dukkan bukatun jama’a su yi masu karatun ta nutsu, wanda za a yi matakin ƙaramar hukumar ayi wanda kuma gwamnatin jiha zata yi a tura mata.
Haka kuma ya bada tabbacin cewa dukkanin abubuwan da jama’a suke buƙata shi za a yi masu, sai dai ya ce buƙatu suna da yawa, saboda haka za a bi su ɗaya bayan domin ganin an cika su kamar yadda jama’a ta buƙata.
Daga karshe ya yi kira da a taimakawa gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa da addu’o’in goyon baya domin samun nasara.
