September 18, 2026

Shugaban Hukumar Yan Sanda Ya Yi Murabus.

0

An bayyana cewa Musiliu Smith wanda tsohon sufeto Janar na ‘yan sanda ne ya yi murabus daga mukaminsa saboda cece-ku-cen da ya biyo bayan daukar dan sanda aiki a rundunar ‘yan sandan Najeriya.

Smith, ana sa ran zai mikawa mai shari’a Clara Ogunbiyi mai ritaya, wacce ke wakiltar bangaren shari’a a hukumar.

Majiyar Popular News Hausa ta jaridar Sunnews ta ce, shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar kula da ayyukan yan sandan Ikechukwu Ani ne ya tabbatar wa manema labarai da batun murabus din shugaban a wata hira ta wayar tarho.

Inda ya yi alkawarin fitar da sanarwar murabus din a gobe Alhamis.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *