Shugaban ƙungiyar kiristocin Najeriya Ya Taya Al’ummar Musulmi Murnar Bikin ƙaramar Sallah a jihar Katsina.
Shugaban ƙungiyar kiristocin Najeriya Reverend Father Shu’aibu ya taya al’ummar musulmi murnar bikin ƙaramar Sallah a jihar Katsina.
Shugaban ƙungiyar ya bayyana hakan ne a cikin sakonshi na Sallah ga ɗaukacin al’ummar Musulmi da ke jihar nan dama ƙasa baki ɗaya.
Malamin ya bayyana bakin Sallah da ke zuwa bayan azumin wata ɗaya a matsayin mai mahimmanci ga bincikar abinda ya gabata domin a gyara abubuwan da ke zuwa.
A madadin al’ummar Kiristocin jihar nan, Reverend Shu’aibu ya yi al’ummar Musulmi barka da Sallah, tare da rokon Allah ya amshi addu’a da ibadar da suka yi a cikin watan azumin.
Ya bayyana bukatar ganin al’ummar Muslimi da kiristoci sun haɗa kansu, sun so juna domin samun cigaba.
Shugaban ƙungiyar kiristocin ya yi kira da a ƙara samun fahimta tsakanin bangarorin 2, tare da jan kunnen su guji faɗa da juna.
Ya yi kira ga Musulmai da kiristoci su tsunduma yin addu’o’in neman zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
Sannan Malamin ya yi kira a yi addu’ar ganin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da ta Dikko Umaru Radda sun samu nasara domin samun romon demokradiyya.
