September 18, 2026

Sarkin Maskan Katsina Ya Yabawa Munkaila Ashafa Akan Ayyukan Ci Gaba A Funtua 

IMG-20260202-WA0004

Daga Hussaini Yero, Funtua

Sarkin Maskan Katsina Hakimin Funtua, Sambo Idris Sambo, ya yabawa tare da jinjinawa tsarin SSA ga Ministan Ayyuka, Alhaji Munkaila Ashafa, bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban garin Funtua da kewaye.

An bayar da shawarar ne a ziyarar da Ashafa ya kai fadar Sarkin Funtua.

Sarkin Maska ya bayyana fitattun ayyukan Ashafa da suka hada da gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana da masallatai da daukar nauyin marayu da bayar da tallafin karatu ga daliban yankin.

“Mutanen Funtua suna godiya da kokarinku, kuma muna addu’ar Allah ya saka muku da alheri.” in ji sarki.

 

Sarkin ya kuma nuna godiyarsa ga jajircewar Ashafa na kawo ci gaba mai kyau ga mutanensa, garinsu, yayin da yake aiki a gwamnati.

 

Sarkin Maska ya kuma bukaci mutanen Funtua da su yi koyi da Ashafa su kuma bayar da gudummawa ga ci gaban al’ummarsu.

About The Author