September 18, 2026

Sarkin Katsina Ya Koka Ma Buhari Kan Janye Kayan Aikin Hanyar Katsina Zuwa Kano.

0

Shugaba Najeriya Muhammadu Buhari ya sake nanata kudurin shi na kammala ayyukan da gwamnatin tarayya ke yi a jihar Katsina.

Shugaban kasar ya bada tabbacin hakan ne a lokacin da ya kai ma sarkin Katsina ziyarar barka da Sallah a fadar shi.

Shugaba Buhari ya sha alwashin ci gaba da kokarin ganin an samar ma kasar nan zaman lafiya.

A nashi bangaren, gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ce cibiyar nazarin masu dauke da cutar daji amincewar gwamnatin tarayya kadai ta ke jira, Popular News Hausa.

Gwamnan ya yi kiran a ci gaba da yin addu’a don samun saukin matsalolin tsaron da Najeriya hadi dama sauran wasu kasashen Afrika na Sahara ke fama da su.

Haka kuma, gwamnan ya yi ta’aziyya ga iyalan Area Commander na yankin Dutsinma da aka kashe bisa sadaukar da kan shi.

Tunda farko, saida sarkin Katsina Abdulmummuni Kabir Usman ya koka ma shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa kwashe kayan da dan-kwangilar dake aikin hanyar Katsina zuwa Kano ya yi, da batun yin watsi da aikin layi dogo na Kano Daura Katsina da kuma aikin samar da wutar lantarki mai amfani da iska ta lambar Rimi.

Abdulmummuni Kabir Usman ya sha alwashin ganin ayyukan sun kammalu duba da mahimmancin su ga al’umma wurin bunkasa tattalin arzuki.

Sarkin dai ya yaba ma shugaban kasa Buhari bisa amincewa da daga darajar asibitin kwararru dake nan Katsina zuwa asibitin koyarwa ta gwamnatin tarayya.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *