Sabon Albishir: Duk Ɗan Jihar Katsina Sai Ya Yi Alfahari Da Gwamnatin Dikko Raɗɗa. -Hauwa Umar Raɗɗa
Hajiya Hauwa Raɗɗa mai ɗakin tsohon shugaban kasar Nijeriya Malam Umaru Musa Yar’adua ta bayyana cewa sannu a hankali mutanen Katsina za su alfahari da wannan gwamnati ta Malam Dikko Umar Raɗɗa.
Hajiya Hauwa ta bayyana haka ne a lokacin da take zantawa da manema labarai a Katsina a ranar Lahadin da ta gabata.
A cewar Hajiya Hauwa gwamna Malam Dikko Raɗɗa, kullum burinsa ya ga jihar Katsina ta samu gagarumin cigaba, mai ɗorewa, sai dai ta ce sai da haɗin kan al’umma za a samu wannan nasara.
“Yanzu Addu’ar da muke ta yi a kullum Allah ya ƙara ba jihar Katsina dawamammen zaman lafiya, saboda duk wani abun cigaba da za’a yi sai da zaman lafiya sannan za a yi shi” inji Hajiya Hauwa
Hajia Hauwa Raɗɗa ta ci gaba da cewa tsakanin mu da al’ummar jihar Katsina sai godiya da irin goyan bayan da suke ba wannan gwamnati ta gwagware
Ta kuma ƙara da cewa abinda Malam Dikko Raɗɗa ya ke buƙata a halin yanzu shi ne muna roƙon Addu’ar su, saboda al’ummar sun aminta da shi ana ganin shi ne mafita, hatta waɗanda suka baro gidajensu akan matsalar tsaro, da yardar Allah kowa zai koma gidansa a samu zaman lafiya mai dorewa a jihar Katsina.
