September 19, 2026

Rikicin APC A Katsina: Idan Ba A Ɗauki Mataki Ba Tana Iya Rudda Ciki A Zaɓen 2023 -Masana

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Sabon rikicin da ya kunno kai a Jami’yyar APC tun bayan kammala zaɓen fidda gwani da aka gudanar na neman zama wata sabuwar hanyar da ka iya kai jamiyyar rijiya gaba duba ( wanda ya faɗa ya tafe ke nan)

Yanzu haka dai masana na cigaba da yin sharhi akan wannan matsala da ta ke neman raba jamiyyar APC gida biyu a jihar Katsina bayan musayar kalamai da ke tada kura daga ɓangarori biyu.

Dakta Kabir Musa Yanɗaki shi ne muƙadashin shugaban tsangayar siyasa a jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina kuma ya jaddada cewa matukar ba a ɗauki mataki cikin sauri ba, makomar APC a Katsina shi ne tana iya dafa ƙasa koma ta yi rudda ciki wato dai faɗuwa zaɓe za a yi.

Ya ƙara da cewa ita jamiyyar a irin wannan lokaci babu abinda take buƙata kamar ɗinke duk wata ɓaraka da rikicin cikin gida domin fuskantar zaɓe da sauran jam’iyyun siyasa da ke dakun karawa da ita.

“Maganar da ma’taimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina Bala Abubakar Musawa magana ce mai tsadar gaske a irin wannan lokaci da ake neman jama’a ba wai a kore su ba kamar yadda ya yi barazana” inji

Bala Abu Musawa dai an ruwaito shi a gaban gwamna Aminu Bello Masari a ƙaramar hukumar Malumfashi Iinda suke je buɗe wasu ayyuka kuma anan ne Bala din ya furta cewa ko APC zata faɗi zaɓe sai sun hukunta waɗanda ke yi halarta wasu tarurruka da suka yi zargin ana cin mutuncin Buhari da gwamna Masari.

Tun kafin Bala Abu ya yi wannan martani tsohon sakataran gwamnatin jihar Katsina kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka nemi takarar gwamnan jihar Katsina bai samu nasara ba ya yi wani taro da kungiyoyi da magoya bayan sa inda ya yi wasu maganganu da ake ganin ya kasa nuna juriya a siyasa.

Daga cikin maganganun da Dakta Mustapha Inuwa ya yi ya ce anci amanar sa, sai dai kai tsaye bai kira sunan wanda ya ci amanarsa ba, amma dai masu sharhi siyasa na ganin kai tsaye wannan magana tasa da gwamna Aminu Bello ya ke.

Sannan Dakta Mustapha ya ƙara da cewa duk wani magoyin bayansa da aka yi wa ba dai dai ba a cikin jamiyyar APC to duk inda ya koma zai taimaka masa, batun da ake ganin kamar ya shirya yi wa jam’iyyar APC zagon ƙasa.

A wani ɓangare na maganganun da suka harzuƙa Bala Abu har ya yi wancan martani akwai wasu kalamai da ɗaya daga cikin dakurun gwagwarmayar neman takarar Mustapha Inuwa tsohon shugaban jam’iyyar APC kuma sakatare a yanzu Malam Shitu Maslaha.

Acikin jawabin da ya yi a wajan wannan taron ya yi takaicin da masu zaɓan fidda gwani suka ƙi zaɓan ɗan takarar shi, inda a ƙarshe ya ce kashi 70 daga cikinsu (delegates) jahilai ne

Malam Shitu Maslaha ya cigaba da cewa daman ya ji tsoron kadda wannan tafiya ta su ta yi irin ƙarkon siyasar Buhari wato ya fara da farin jini amma zai kare da zagi, waɗannan kalamai da Dakta Mustapha Inuwa da Shitu Maslaha sune musababin wancan magana ta Bala Abu Musawa.

Kamar yadda Dakta Kabir Musa Yanɗaki ya faɗa cewa ita jami’yya tana da tsarin da yake bi wajan hukunta ‘ya ‘yan ta idan sun yi ba daidai ba, amma maganar cewa ko za a faɗi zaɓe sai an hukunta masu halartar irin wancan taro ba daidai ba ne a siyasa

Ya kuma ƙara da cewa wannan rikicin cikin gida ne wanda ya kamata ace gwamna Aminu Bello Masari ya yi wa tufkar hanci tun kafin abin ya yi nisa, inda ya ce idan aka cigaba wannan rikicin cikin gida, to ƙarshe magana shi faɗuwa zaɓe za a yi ba tare da wata tantanma ba.

A cewar Dakta Kabir Musa Yanɗaki su sauran jam’iyyu wannan faɗan yana yi masu dadi kuma ba sa so ya kare domin idan aka cigaba su za su ci amfann shi ta hanyar yiwa jam’iyyar APC dukkan kawo wuka a ranar zaɓen 2023

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *