September 17, 2026

Ranar Sojoji: Gwamna Raɗɗa Ya Yabawa Dakarun Soji Kan Jajircewa da Sadaukarwa Wajen Yaƙi da Rashin Tsaro

FB_IMG_1783350717708

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya taya jami’ai, dakaru da tsoffin sojojin rundunar sojin Nijeriya murnar bikin ranar sojojin Nijeriya ta shekarar 2026

 

Gwamna Radda ya bayyana taken bikin na bana, “kare ƙasa da yi wa al’umma hidima,” a matsayin wanda ya dace da irin jajircewa da sadaukarwar rundunar sojin Nijeriya wajen kare martabar ƙasar nan tare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

 

Haka kuma ya yaba matuƙa da jarumtaka, ƙwarewa da sadaukarwar jami’ai da dakarun rundunar sojin Nijeriya, musamman waɗanda ke aikin tabbatar da tsaro a sahun gaba a jihar Katsina, yankin arewa maso yamma da sauran sassan ƙasar da ke fama da matsalar rashin tsaro.

 

Kazalika ya jinjinawa rundunar kan ƙoƙarint a na yaƙi da ‘yan bindiga, ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyukan, yana mai cewa jajircewar su na ci gaba da ƙarfafa tsaron ƙasa tare da dawo da fata ga al’ummomin da matsalar ta shafa.

 

Gwamna Raɗɗa ya sake jaddada ƙudirin gwamnatin sa na ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da rundunar sojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa a faɗin jihar.

 

“Gwamnatin mu na ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa rundunar sojin Nijeriya ta hanyar ƙarfafa haɗin gwiwa, musayar bayanan sirri da kuma haɗa kan al’umma. Tare za mu ci gaba da ƙarfafa yaƙi da rashin tsaro ha kuma za mu samar da yanayi mai aminci da jama’ar mu za su rayu, su yi aiki kuma su bunƙasa.” Inji shi

 

Gwamnan ya kuma tuna da jaruman jami’ai da dakarun da suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare ƙasa, inda ya yi addu’ar Allah Ya jikansu da rahama, sannan ya yi fatan Allah ya baiwa waɗanda suka jikkata lafiya

 

About The Author