September 17, 2026

Ramadan: Yadda Gidauniyar Dakta Kabir Magaji Gafia Ta Raba Miliyan 18 Ga Mutane 727 a Katsina.

IMG_2617

Aƙalla Mutane 727 ne fa suka fito daga bangarori daban-daban a karamar hukumar Kaita suka amfani da tallafin gidauniyar Kabir Magaji Gafia da zunzurutun kudi har naira miliyan 18

 

Tallafin dai na da nufin yin amfani da shi a wata mai alfarma wato watan Ramadan da ke tafi wanda haka shi ne karo na biyu da aka gudanar da irin wannan tallafi

Gidauniyar dai na ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar ilimin ɓai daya na jihar Katsina Dakta Kabir Magaji Gafia.

 

Da yake magana a madadin gwamnan jihar Katsina, sakataren gwamnatin Katsina Barista Abdullahi Faskari ya yaba da wannan kokari wanda ya ce an bukatar haka a daidai wannan lokaci.

A cewar sa, wannan tallafi zai taimaka matuƙa gaya wajen rage radadin da al’umma ke fama da shi na rayuwa musamman watan azumi da ke tafe

 

Daga nan sai ya yi kira ga wadanda suka amfana da wannan tallafi da su yi amfani da shi yadda ya da ce, tare da fatan suna za su taimakawa wasu ko ya ya ne

 

Tunda farko da yake jawabi shugaban gidauniyar Dakta Kabir Magaji Gafia ya bayyana cewa wannan tallafi wani ɓangare na nuna damuwa da abubuwan da suka shafi al’umma na gwamna Raɗɗa musamman masu buƙata ta musamman.

Saboda haka ne ya yi kira ga wadanda suka amfana da wannan tallafi da su yi amfani da shi cikin watan azumi da zai kama.

 

Yana bayyana cewa an tsara daki-daki yadda za a raba waɗannan kuɗaɗai ga mutane 727 da suka fito daga ƙaramar hukumar Kaita.

 

A cewar Dakta Kabir Magaji, daga cikin waɗanda za su amfana akwai masu buƙata ta musamman da ‘yan jam’iyyar su ta APC da mata da matasa da kungiyoyi.

 

Sauran sun haɗa da limamai da masu rike da sarautar gargajiya da masu rike da muƙamai domin su shiga watan Ramadan cikin farin ciki

 

Sai dai Dakta Kabir Magaji ya ce wannan tallafi da ya bada ba yana neman kowane irin mukami ba ne, ya yi ne domin wannan hanyar ce gwamna Raɗɗa ya ɗora su a kai.

“Yanzu wannan tallafi ba rancen ba ne nake badawa ba, bashi ne nake biya, saboda haka abinda kawai zan nema anan gaba shi ne al’ummar ƙaramar hukumar Kaita su yi abinda suka saba, wato ruwan kuri’a idan zaɓe ya zo ga gwamna Raɗɗa da sauran ‘yan takara” inji shi

 

Daga karshe ya yi fatan Allah ya maida kowa gidan sa lafiya ya kuma nuna mana shigowar wata mai albarka watan Ramadan.

About The Author