Mutum 2 Sun Shiga Hannu Akan Zargin Yin Garkuwa Da Mahaifiyar Rarara a Katsina
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta kama mutum 2 da ake zargin suna da hannu wajen sace mahaifiyar shaharar mamakin Dauda Abdullahi Kahutu Rarara.
Kakakin rundunar ‘yan Sanda ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar aka rabawa manema labarai a Katsina.
Rundunar ta ce, mutanen biyun da aka kama bisa zargin hannu suna amsa tambayoyi ne a rundunar inda ta ce daga baya zata sanar da cigaban da aka samu akan lamarin
Tunda farko sai da ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce baturan ‘yan sanda na ƙaramar hukumar Danja ya jagorancin jami’an tsaro zuwa wajen da lamarin ya faru domin kama waɗanda ake zargi da aikata laifin.
Ya ƙara da cewa ‘yan sanda sun yi nasarar dake mutane biyu da yanzu haka suke amsa tambayoyin a hannun jami’an tsaro.
An sace mahaifiyar shaharar mamakin siyasar nan Alhaji Dauda Abdullahi Kahutu Rarara Hajiya Halima yar shekara 75 a daren jiya alhamis a garin Kahutu da ke karamar hukumar Danja ta jihar Katsina.
ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce bincike akan wannan lamari na cigaba da gudana sannan ya bada tabbacin kamo waɗanda suka yi wannan ɗanyen aiki.
