Mustapha Inuwa Ga Ɗaliban Aikin Jinya: Ku Maida Hankali Wajan Karatun ku Saboda Gaba
Daga The Fact 24
Kwalejin Koyon Aikin Jinya Da Ungozoma da Marigayi Abba Sayyadi Ruma ya Kafa, ta gudanar da Bikin Rantsar da Sababbin Dalibai karo na farko.
Bikin Rantsar Da Daliban da ya gudana a Harabar Makarantar da ke GRA Katsina, ya samu halartar iyaye da yan uwa gami da masu kyakkyawan fata ga daliban.
Babban Bako a wurin Bikin kuma Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa, ya taya daliban murna akan wannan dama da suka samu ya yin karatu a Kwalejin.
Alhaji Mustapha Inuwa ya yaba da irin Kokarinda Kwalejin ke yi wurin bada gudummuwa ga inganta kiwon lafiya da Ilimi a Jihar Katsina.
Daga nan sai ya hori daliban akan su kasance masu mayar da hankali akan karatunsu lura da cewar idan sun Kammala karatunsu zasu rika kula da lafiyar al’umma.
Sauran wadanda suka maganta a wurin taron rantsar da sababbin daliban sun hada da Shugaban Hukumar Gudanarwa na Kwalejin da Kuma Shugaban Makarantar da dai sauransu.
Sun nanata kudirin Kwalejin na cigaba da yin bakin kokarinta ta fuskar samar da nagartaccen Ilimi ga daliban ta.
A lokacin taron an gabatar da Kyaututtuka ga wasu dalibai da malamai da suka bada kwazo.
