RANAR MATA TA DUNIYA: Lokaci Ne Don Bunƙasa Tunanin Mata a Jihar Katsina
Ranar Mata ta Duniya lokaci ne na murnar nasarorin da mata suka samu tare da yin nazari kan kalubalen da suke fuskanta, musamman a Jihar Katsina inda mata da yara ke fama da matsaloli kamar rashin tsaro, talauci, yunwa, rashin ingantaccen Muhalli da kuma yan gudun hijira.
Bincike ya bayyana cewa mata da dama suna rayuwa a matsayin ’yan gudun hijira ba tare da wadatattun bukatun rayuwa ba, yayin da rashin tsaro ke kara lalata rayuwarsu tare da daƙile ci gaban rayuwar su. Jinkina wa mata kan wahalhalun da suke sha da kuma yabama juriyarsu.
Kara karfafa ayyukan kungiyoyin tallafi kamar NGOs, CBOs da CSOs da ke samar da abinci, ilimi, Muhalli da tallafin lafiyar su,
tare da Kafa manufofi da dokoki masu karfi domin magance matsalolin rashin tsaro, yunwa da muhalli.
Samar da wata kafa da zata baiwa mata damar bayyana matsalolin su domin samun mafita.
A karshe, muna kara kira ga hadin kai tsakanin gwamnati, kungiyoyin tallafi da shugabannin al’umma domin tabbatar da tsaro da walwalar mata da yara, tare da jaddada cewa bikin Ranar Mata ya kamata ya zama hanyar kawo sauyi mai anfani ga rayuwar mata da yayansu.
Amb Khadija Sulaiman saulawa
Deputy chairman (NYCN) founder of (Queen Dijah Initiative)
