September 18, 2026

Jami’an Tsaron Nijeriya Na Yi Mana Barazana a Jihar Katsina – Almajiran Sheikh Zakzaky

IMG_20260316_202107_498

 

Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky a jihar Katsina sun zargin jami’an tsaron Nijeriya da yi masu barazana saboda sun nuna goyon bayan su akan yaƙin da ake gwabzawa tsakanin Amurka da Israel da kuma jamhuriyar Musulunci ta Iran

 

Wannan zargin dai ya biyo bayan ganin tawagar jami’an tsaro sun yi wa mabiya Sheikh Zakzaky ƙawanya a daidai lokacin suka fito muzaharar nuna goyon baya ga jamhuriyar Musulunci ta Irana satin da ya gabata

 

Sheikh Shehu Ɗalhatu ne ya bayyana haka a madadin sauran almajiran Sheikh Ibrahim a lokacin da ya kira wani taron ‘yan jarida a Katsina

 

Shehin Malamin ya cigaba da cewa suna zargin shugaban ‘yan sandan Nijeriya ne ya bada umurnin a cigaba da sanya ido a duk wani motsin ‘yan uwa almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky a Nijeriya baƙi ɗaya.

 

Sheikh Usman Ɗalhatu Ƙarƙarku ya ƙara da cewa sun ga motocin jami’an tsaro fiye da 20 masu suke ɗauke da muggan makamai suna sintiri cikin birnin Katsina.

 

A cewar sa, irin waɗannan jami’an tsaro kamata ya yi a ce suna daji domin kawar da ɓarayin daji da suka addabi al’umma, amma abin mamaki sai ga su cikin garin suna kokarin tada hankalin jama’a.

 

“Idan muka duba alaƙar da ke tsakanin Nijeriya da ƙasa Israel ce ta sanya har jakadan su ya fito fili yake zargin cewa wai harka islamiyya ƙarƙashin Sheikh Ibrahim Zakzaky ana horas da ‘yan ta’adda a Nijeriya” inji shi

 

Ya ƙara da cewa gudunmawar da za su iya badawa akan wannan yaki da ake gwabzawa shi ne yin muzaharori na nuna goyon baya da kuma addu’o’i saboda a cewar sa duk duniya ana yin haka.

 

Sheikh Usman Ɗalhatu Ƙarƙarku ya ce amma a Nijeriya duk da dokar ƙasa ta bada ‘yancin yin muzahara amma ana neman tauye masu ‘yancin su na ‘yan ƙasa.

 

Kazalika ya yi kira ga gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin Dikko Umar Raɗɗa da masu ruwa da tsaki a jihar da cewa duk wani da ya faru to su zargi jami’an tsaro.

 

A cewar sa, alamu sun nuna yadda jami’an tsaron Nijeriya ke mararin sheƙar da jinanan almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky a jihar Katsina musamman ganin lokacin yin muzaharar Kudus ya gabato.

 

“Mun sha yin muzaharorin mu fiye da shekaru 30 muna yi, mu gama lafiya ba tare da an kashe ko da kiyashi ba, ko an ɓarnata dukiyar kowa ba, su al’ummar Katsina shaida ne akan hakan” inji shi

 

Saboda haka yake ƙara jan hankalin al’umma musamman na jihar Katsina cewa idan an ga wani abu ya faru ba daidai ba, to lallai jami’an tsaro ne ke da alhakin aikata haka.

About The Author