Muna Faɗuwa Zaɓe Rushe Ku Za A Yi: Jan Kunnen Dikko Raɗɗa Ga Mataimakan Ciyamomin Katsina
Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyyar APC Dakta Dikko Radda ya gargaɗi Mataimakan shuwagabannin ƙananan hukumomin da su yi duk mai yiyuwa wajan ganin APC ta sake kafa mulki a jihar Katsina.
Dikko Umar yana wannan magana ne a lokacin da Mataimakan Ciyamomin suka kawo masa ziyarar mubayi’a tare da nuna goyon baya a wannan tafiya tasa.
Ɗan takarar wanda ya ce idan Allah ya kawo wani iftila’i cewa 2023 jam’iyyar APC ba ita ke da gwamnati ba, Dikko ya ce kowanensu sai ya shirya jikkunansu domin sun san dai rushe su za a yi.
“Wannan abu da zamu yi jam’iyyar APC zamu yi wa, yau magana ce ta jami’yya ko kana san mutum ko baka san shi, tunda Allah ya bashi takara a ƙarƙashin jam’iyar APC ya zama wajibi gare ka ka goyi bayan shi” in ji Dikko
Ya ƙara da cewa idan kana gwamna ka rasa shugaban ƙasa kana cikin matsala, idan kana Ciyaman ko ma’taimaki ko kansila ka rasa gwamna a jihar ka kana cikin matsala, ya ce ya zama wajibi gare su da su tashi tsaye domin yi wa jam’iyyar APC aiki don ganin an samu nasara.
Popular News Hausa ta ruwaito cewa ɗan takarar ya yi kira da babar murya akan cewa kowa sai ya bada rayuwarsa da dukiyarsa ya ce ta haka ne idan aka samu nasara su ma ta su dukiyar zata tsira.
Daga ƙarshe ya yi godiya ga mataimakan shuwagabannin ƙananan hukumomi bisa wannan ziyara ta nuna goyon baya a wannan tafiya ta shi.
Wasu daga cikinsu da suka yi jawabi a madadin sauran sun bada tabbacin cewa za a yi wannan tafiya da su domin cimma nasarar da aka sa gaba
Popular News Hausa
