Mota Ta Kubce Tare Da Kashe Mutane 3 Wurin Da Ake Sayar Da Jaridu.
Labarin ya afku ne a garin Warri dake jihar Delta a makon jiya, lokacin da wata mota fara kirar Range Rover Jeep mai lamba kamar haka: Delta EFR 940 TT ta kutsa wurin sayar da jaridar dake shatale-talen Iyara a yankin, inda ta kashe mutane uku, yayin da daya ya samu rauni.
Wani ganau da ya shaida wa wakilin jaridar Leadership yadda labarin ya faru, ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da direban motar dake gudu ta kubce mashi, kuma ya rasa yadda shai shawo kan motar inda ya kashe masu karatun jaridar uku nan take.
An bayyana cewa, direban ya samu munanan raunuka, saidai mata biyu dake cikin motar ba su samu rauni ba. An ga jami’an ‘yan sanda na gudanar da bincike akan hadarin lokacin da wakilin jaridar Leadership ya isa wurin da lamarin ya faru, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Leadership.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Delta, DSP Bright Edafe bai ce komai akan tambayoyin da aka aike mashi ba.
