Menene Makomar Hon. Shehu Abdu Daura Da Kotun Majistire ta wanke Akan Zargin Da Ake Yi mashi?
An yanka ta tashi, Kotu ta wanke ɗan takarar shugabancin ƙaramar hukumar Daura, wanda shine ya lashe zaɓen fitar da gwani da aka gudanar ƙarƙashin Jama’iyyar APC wato Hon. Shehu Audu Daura.
Idan Mai karatu bai manta ba dai Biyo bayan nasarar zaɓen da yayi ne, aka samu ƙorafe ƙorafen cewa wai ya amshi kuɗaden wasu Yara da niyyar samar masu guraɓen ayyuka kuma ya cinye kuɗaɗen ba tare da ya samar masu aikin ba.
Ƙarar dai ta fito ne daga Ma’aikatar Shari’a ta jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin tsohon babban lauyan jihar, wanda ta sanadiyyar hakan aka kulle Hon. Shehu na tsawon sama da wata guda har sai bayan da lauyoyin shi suka shigar da ƙara babban kotun jiha wadda ta badashi beli.
Yanzu dai kotun da aka shigar da ƙarar shi ta wanke shi bayan kimanin watanni Huɗu da fara wannan danbarwar da ake ganin akwai kullaliya da sa hannun wasu acikin ta, saboda dalilai na siyasa.
Abun tambaya anan shine shin yanzu da yake kotu ta wanke shi ko zai koma kai tsaye ya amshi ragamar jagorancin ƙaramar hukumar Daura tunda shine Halastaccen ɗan Takarar da Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta baiwa katin shaida?
