Mauludi : Duk Da Ruwan Sama ya hana taro Amma na ga taron Masoya Annabi- Sayyada Raihan Imam Ƙamshi
DAGA MUKHTAR YAKUBU
A sakamakon wani ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a birnin Kano da kewaye a ranar asabar 20 ga Satumba, hakan ya kawo tsaiko ga taron bikin Mauludin Manzon Allah S A W, da Sayyada Raihan Imam Kamshi ta saba gabatarwa a duk shekara.
An dai tsara za a fara taron Mauludin ne da misalin karfe 7 na yamma zuwa abin da ya sawwaka. Hakan ya sa komai ya kammala na taron Mauludin an tsara wajen da rumfuna da kujeru na alfarma ga Darduma masu ɗaukar hankali da aka shirya a wajen manyan baki da sauran abubuwan da suke ƙayatar da wajen taro.
Sai kuma aka samu saukar ruwan sama tun daga karfe 6 har zuwa tsakiyar dare. Wannan ya sa komai na taron ya tsaya ana jiran lokacin da ruwa zai tsaya, amma ruwan sai ci gaba ya rinƙa yi babu kakkautawa, kuma daman ga shi Iska ta wargaza wajen don haka taron ya kasa yiwuwa.
Sai dai duk da haka dumbun jama’a masoya Manzon Allah S A W, sun yi ta zuwa a cikin ruwan domin nuna shaukin su ga taron Mauludin, don haka jama’a suka taru a cikin gidan su Raihan Imam Kamshi har zuwa Kofar gida taron mutane ne babu masaka tsinke.
Jama’a sun taru da Malamai Sha’ir ai ‘yan fim da sauran jama’ar gari, duk wanda ka gani a jike yake, sai dai wanda ya saka rigar ruwa.
Dangane da yadda taron bikin Mauludin na bana ya kasance, mun nemi jin ta bakin Raihan Imam Kamshi, musamman yadda ruwan sama ya canza fasalin taron.
Ga shi dai yau kika tsara za ki gudanar da taron Mauludin ki, kuma ruwan sama ya sauka ana ta yi har tsakiyar dare ko ya kika samu kan ki a wannan lokacin?
To Alhamdulillah! Ka ga dai yadda taron ya zama mun gama shirya komai an hada waje an saka duk abin da ya kamata a saka , muna daf da mu fara sai aka samu saukar ruwan sama mai karfi da Iska, hakan ya sa wajen ya lalace don abubuwan da aka kafa Iska da ture su, wasu abubuwan da aka lika Iska ta yage su. Tun muna tunanin za a ɗauke ruwa mu yi da abin da ya samu sai ruwa bai dauke ba.
Ga kayan da za mu raba a wajen, ga abinci da za a raba duk an kammala domin akwai kyautuka da za a raba wa Masoya Annabi da za su halarci wajen, sai dai yanayin saukar ruwan saman bai sa abin ya tafi a yadda muka tsara ba, kuma wannan al”amari ne na Allah, shi ya ke tsara yadda ya so a lokacin da ya so.
Hakan ne ya sa komai ya tsaya kenan?
To ba za a ce komai ya tsaya ba. Duk da haka babu abin da zan ce da Allah sai godiya. Domin kuwa duk da ruwan da aka yi Jama’a Masoya Manzon Allah S A W sun halarci wajen fiye da yadda nake tunani.
Ana ruwa mutane suna ci gaba da zuwa Unguwar mu ta cika da motocin mutane masu zuwa wajen Mauludin wasu sun saka rigar ruwa ,wasu kuma babu rigar ma haka suka taho a jike, duk wanda ka gani a wajen a jike yake.
Tun ana shiga cikin gida, sai gidan ya cika mutane suka rinka tsayawa a waje nan ma dai layin namu ya cika.Kai abin dai sai godiya ga Allah, domin lamarin Annabi daban ne. Ni kaina na yi mamakin kaina duk da ba na son shiga ruwa haka na fito ina taryar baki cikin ruwan na jike sharaf, saboda mutane zuwa suke har zuwa karfe 1 na dare, wanda ko da taron Mauludin ma za a yi to iya lokacin da za a tashi kenan.
Ko wanne darasi kika samu a wannan taron Mauludin?
To gaskiya na samu darasi sosai, domin ka ga duk shekara na saba shirya taron Mauludin a duk ranar 27 ga Rabi’ul Awwal amma ba a samu lokacin da ya hade da ruwan sama ba sai na wannan shekara, to ka ga wannan darasi ne da yake nuni da ita rayuwa ba ko da yaushe abin da ka shirya ko kake so kuma yake samuwa ba.
Idan son samu na ne na yi taron Mauludin kamar yadda na tsara , sai kuma Allah ya sa ruwa ya sauka, kuma na yi shiri sosai a wannan shekarar fiye da yadda na saba yi a baya. Su kan su Jama’ar a yadda na gani da ba a samu saukar ruwan ba, to yawam su sai ya fi na baya, ka ga wannan ma darasi ne.
Muna fatan Allah ya kaimu na shekara mai zuwa cikin koshin lafiya.
Kuma Ina godiya ga manyan Malamai da suka halarci wajen taron duk da ruwan da aka yi. Haka nan Sha’irai su ma na gode sosai Allah ya kara kusanci da Annabi.
Su ma abokan sana’a ta ‘yan fim da daman su sun zo don haka ina godiya a gare su, Allah ya bar zumunci, Allah ya kara mana son Manzon Allah S A W.
To Madalla mun gode.
Nima na gode sosai.
