Matsalar Tsaro: Ta Kan Iyakoki Ake shigowa Da Makamai Nijeriya. -Gwamna Dikko Raɗɗa
Matsalar Tsaro: Ta Kan Iyakoki Ake shigowa Da Makamai Nijeriya. -Gwamna Dikko Raɗɗa
Daga Hussain Yero, Funtua
Gwamnan jihar Katsina Dikko Raɗɗa, ya jaddada buƙatar gwamnati ta ƙara tsaurara matakan tsaro da Kyakkywar kulawa akan iyakokin ƙasar nan domin a cewar sa ta nan ne ake shigowa da Makamai.
Haka kuma ya bayyana cewa dole ne a yi yaki da cin hanci da rashawa, wanda ya dabaibaye shuwagabani da cin amanar al’umma idan aka magance waɗannan abu zai taimaka matuƙa wajen magance matsalar rashin tsaro a ƙasar nan.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da lacca ta biyu na bikin amsar sabin ɗalibai A Jami’ar Tarayya da ke Gusau, A juya juma’a
Gwamna Raɗɗa ya bayyana jahilci cin hanci da Rashawa ga shugabanni da shugabanci, rashin yarda da addini da shaye-shayen miyagun kwayoyi na daga cikin manyan abubuwan da ke kawo taɓarɓqarewar tsaro da ke kawo illa ga ci gaban ilimi a kowace nahiya.
Gwamna Raɗɗa ya ce, yawaitar satar yara ‘yan makaranta da ‘yan gudun hijira na haifar da rashin zuwa makaranta, wanda anan gaba zai zama illa ga Kasar nan.
“Akan haka ne Gwamna Raɗɗa yayi kira ga shugabanni da suji tsoran Allah akan amanar da suka ɗauka na kare al’umma da ilmantar da su da kuma ba jami’an tsaron mu Kyakkywar kulawa musamman masu kula da kan iyakokin shigowa ƙasar nan.yin haka shine zai taimaka wajan dakile matsalar tsaron da ta’adabi m’ .inji
