September 18, 2026

Masu Ruwa Da Tsaki Na Jam’iyar APC A Katsina Sun Kafa Wasu Kwamitoci Domin Gudanar Da Zaɓukan Ƙananan Hukumomin Jihar.

0

Taron masu ruwa da tsakin wanda ya gudana a ɗakin taron shugaban ƙasa da ke gidan gwamantin jihar Katsina, ya samu halartar tsaffin gwamnoni 2 Aminu Bello Masari da Barrister Ibrahim Shehu Shema.

A jawabanshi lokacin taron, gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa mataimakinshi Faruk Lawal Jobe zai shugabanci kwamitin kula da zaɓe, sakataren gwamnatin jihar Katsina Barrister Abdullahi Garba Faskari zai jagoranci kwamitin gudanarwa da tantancewa, yayinda tsohon mataimakin gwamnan jihar Katsina Tukur Ahmed Jikamshi zai jagoranci kwamitin ɗaukaka ƙara.

A ɗayan ɓangaren kuma, kwamitin sasanci zai kasance ƙarƙashin shugabancin babban mai taimakawa shugaban ƙasa akan harkokin siyasa Kabir Ibrahim Masari.

Kamar yadda ya bayyana, an kafa kwamitocin tantancewa na shiryar Katsina, Daura da Funtua.

Ya ce Yahaya Idris A-Sasanta shi ne zai shugabanci kwamitin Katsina, Mudassiru Mati zai shugabanci na Daura, yayinda Ibrahim Danjuma zai shugabanci na shiryar Funtua.

Gwamna Dikko Radda wanda ya ce kwamitocin sun fara ayyukansu, saidai ya ce an yima jaddawalin farko kwaskwarima domin samar da lokacin shirya ma zaɓukan.

Masu ruwa da tsaki na jam’iyar APC a Katsina sun kafa wasu kwamitoci domin gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomin jihar da ke tafe cikin kwanciyar hankali.

Taron masu ruwa da tsakin wanda ya gudana a ɗakin taron shugaban ƙasa da ke gidan gwamantin jihar Katsina, ya samu halartar tsaffin gwamnoni 2 Aminu Bello Masari da Barrister Ibrahim Shehu Shema.

A jawabanshi lokacin taron, gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa mataimakinshi Faruk Lawal Jobe zai shugabanci kwamitin kula da zaɓe, sakataren gwamnatin jihar Katsina Barrister Abdullahi Garba Faskari zai jagoranci kwamitin gudanarwa da tantancewa, yayinda tsohon mataimakin gwamnan jihar Katsina Tukur Ahmed Jikamshi zai jagoranci kwamitin ɗaukaka ƙara.

A ɗayan ɓangaren kuma, kwamitin sasanci zai kasance ƙarƙashin shugabancin babban mai taimakawa shugaban ƙasa akan harkokin siyasa Kabir Ibrahim Masari.

Kamar yadda ya bayyana, an kafa kwamitocin tantancewa na shiryar Katsina, Daura da Funtua.

Ya ce Yahaya Idris A-Sasanta shi ne zai shugabanci kwamitin Katsina, Mudassiru Mati zai shugabanci na Daura, yayinda Ibrahim Danjuma zai shugabanci na shiryar Funtua.

Gwamna Dikko Radda wanda ya ce kwamitocin sun fara ayyukansu, saidai ya ce an yima jaddawalin farko kwaskwarima domin samar da lokacin shirya ma zaɓukan.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *