Majalisa ta amince da hukuncin daurin rai da rai ga masu ta’mmali da miyagun kwayoyi
Majalisa ta amince da hukuncin daurin rai da rai ga masu ta’mmali da miyagun kwayoyi
Majalisar Dattawa ta yi gyaran dokar Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), inda ta tanadi hukuncin daurin rai da rai ga masu ta’ammali da miyagun kwayoyi da masu fataucinsu.
Wannan shawara ta biyo bayan karɓar rahoton haɗin gwiwa na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai kan gyaran dokar NDLEA.
Yayin gabatar da rahoton, Shugaban Kwamitin Haɗin Gwiwa na Majalisar Dattawa, Sanata Tahir Monguno, ya bayyana cewa gyaran dokar ya nufi ƙara tsauraran hukunci don hana ayyukan miyagun kwayoyi da fataucin su.
Majalisar Dattawa ta amince da wannan shawara ta hanyar kada kuri’ar baki a zauren ranar Alhamis, wanda Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya jagoranta.
