September 18, 2026

Kwana 100 Da Mulkin Dikko Raɗɗa: Jama’a Ku Bada Goyon Baya Domin Cimma Nasara. Hon. Isah Muhammad Kankara

0

Kwamishinan Ayyuka na Musamman a jihar Katsina, Alh. Isa Mohammed Musa Kankara ya yi kira ga al’ummar jihar nan da su cigaba da nuna goyon bayan su ga gwamnatin Malam Dikko Umaru Raɗɗa.

Alh. Isa Mohammed Musa Kankara yayi wannan kira ne a dai dai lokacin da gwamnatin Malam Dikko Raɗɗa ke cika kwanaki 100 a kan karagar mulki.

Kwamishinan yace a cikin kwanaki 100 da wannan gwamnati tayi, an samar da tsare-tsare masu kyau a fannonin tsaro, Ilimi da sauran ayyukan raya qasa don cigaban Jahar nan.

Daga cikin su akwai ɗaukar matasa don basu horo don tunkarar ayyukan ta’addanci, bayar da tallafi ga iyalan waɗanda ayyukan ta’addanci ya rutsa da su, mayar da yan’ S-Power malamai na din-din-din da sauran ɓangarori daban-daban

Daga ƙarshe yayi godiya ga Malam Dikko Raɗɗa bisa damar da ya bashi don bautawa jihar Katsina a matsayin kwamishina, tare da yin addu’a ta Allah ya cigaba da taimakawa gwamnan a ƙoƙarin da ya keyi na kawo cigaba mai ɗorewa a jihar Katsina.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *