September 18, 2026

Kwamitin Yi Wa Ƙasa Addu’o’i Ya yi Kira da Al’ummomi Da Su ƙara Hakuri da Juna Da Fifita Zaman Lafiya

0

Kwamitin Yi Wa Ƙasa Addu’o’i Ya yi Kira da Al’ummomi Da Su ƙara Hakuri da Juna Da Fifita Zaman Lafiya

Wata kungiyar yiwa ƙasa addu’a da ta kunshi al’ummar Musulmi da kirista tayi kira kan buƙatar kaucewa banbancin addini da dukufa yin addu’oi da neman agaji daga Allah kan matsaloli da su kayi dabaibayi wa ƙasar nan.

Wani kwamitin Amintattu kan yiwa ƙasa addu’oi wacce ta dukufa kan yiwa kasa addu’oin Samun salama da kwanciyar hankali , ta jinjina wa Gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu a bisa yankurin ta na samar da cigaban rayuwa.

Kungiyar ta kuma miƙa kwafin littattafan Qur’ani mai girma da Bible mai tsarki ga mashawarci na musamman ga shugaban ƙasa kan al’amuran tsaro, Mallam Nuhu Ribado a birnin tarayya Abuja, a matsayin wata hanya ta anfani da addu’a wajen magance ƙalubale da ke zama tarnaki wa ƙasa Nijeriya.

Sakataren kungiyar, Mallam Auwal Yakasai ya jaddada yunkurin kungiyar na cigaba da yaɗa busharar zama da juna lafiya kyautata jagoranci na kwarai da tafiya da kowa da kowa da gwamnatin ta ke faɗi tashin tabbatar wa mulkin ta.

A cewar sa an shirya ganawar ce da zimmar tabbatar da fahimtar juna da hadin kan ƙasa da kuma nusar da masu yunkurin kawo tarnaki ga cigaban ƙasa, yayi nuni da cewa a yanzu lokaci wuce da banbancin addini da siyasa da ɓangaranci wanda hakan ke haifar da zaman doya da manja tsakanin jama’ar ƙasa.

Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar, Alhaji Sunusi Baban Takko (Barayan Bauchi) da kuma Darakta janar na kungiyar S.B Afolorunnikan su ne suka jagoranci tawagar kungiyar domin mika kwafin littattafan masu tsarki ga mashawarci na musamman ga shugaban ƙasan kan sha’anin tsaro, suka ce kwamitin amintattun yayi maida hankali be wurin shirya yiwa kasa addu’a domin ɗorewa zaman Lafiya da ,cigaba mai d ɗorewa a daidai lokacin da gwamnatin shugaba Tinubu ke cika shekara guda akan mulki.

Kwamitin ya yi amannar cewar jajircewar gwamnatin tarayya ta fuskar Gina Dan Adam, farfado da tattalin arziki da yaji da talauci sun fayyace alkiblar da gwamnati tasa gaba a cikin shekara daya kachal.

Da yake karɓan bakuncin tawagar, a madadin mashawarci na musamman ɗin Abdul aziz – Abdul Aziz hadimi ga shugaban ƙasa kan yada labarai kuma wanda mamba ne a kungiyar, yayi alkawarin Isar da dukkanin buƙatu na kungiyar domin bata damar cimma kudurorin ta na tabbatar da wanzar da zaman lafiya haɗin ƙasa da Samar da cigaba mai ɗorewa.

Cikin waɗanda suka halacci taron sun haɗa da Mallam Ibrahim Khalifa, Babban limamin masallacin Ɗantata da ke Abuja, Mallam Mahadi, mamba a kwamitin Babban masallacin ƙasa, da Hon. Ibrahim Marmara gami da Pastor Joseph Dihis

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *