Kwamishinan ‘Yan Sanda Na Jihar Kano Ya Kaiwa Hukumar Kwastan Da DSS Ziyarar Aiki
Daga Babangida Sunusi, Kano
A ranar larabar wannan makon ne kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano ya kaima takwarorinsa na hukumar hana fasa kwabri mai kula da shiyar Kano da Jigawa da kuma hukumar farin kaya wato SSS ziyarar aiki.
Kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar Yan sandan jihar Kano SP Haruna Abdullah Kiyawa ya fitar ga manema labarai.
Da yake jawabi yayin ganawa da shugabanin hukumomin biyu kwamishinan CP Abubakar Lawal Daura yace ya ziyarci ɓangarorin guda biyu ne dan gabatar da kansa tareda neman goyon bayan wannan hukumomi dan samun nasarar aiki tare da samar da kyakkyawan tsaro a jihar kano.
Shima a nasa jawabin lokacin da ya karɓi kwamishinan kwantrolan hukumar mai kula da shiyar Kano da Jigawa Mu’azu Hassan Raji, ya yi wa kwamishinan barka da zuwa da sauran ‘yan tawagarsa, inda yaka dacewa kasancewar iri ƙoƙarin kwamishinan da yake yana ganin akwai damar koyi daga gareshi dan haka babu wata hukumar tsaro da zatai aiki tasamu nasarar bada hukumar Yan sanda ba, dan haka za su duk mai yuwuwa dan haɗa gwiwa wajan maida Kano Kan turbar mun tsira.
Kazalika shima da yake karɓar kwamishinan yayin ziyarar shugaban hukumar ta farin kaya na jihar kano Alhaji Hassan N.Mohammed yayi matukar godiya da wannan ziyarar aiki da shugaban hukumar ta Yan sanda na Kano yakawo masu.
Dan haka matsayin su na jami’an sirri suna taka mahimmiyar rawa tareda da jami’an Yansanda dasuke kan gaba wajen bada cikakken bayan sirri, Hassan yace lallai zasu cigaba da ba hukumar Yan sanda goyon baya da aiki tare dan samun nasara.
