September 18, 2026

Kwamarad Mannir Suleiman Ya Mamba A Kungiyar Malaman Kiwon Lafiya Ta Kasa

IMG-20241207-WA0048_1

Kungiyar Malaman Kiwon Lafiya da unguwar Zoma ta amince da naɗa tsohon shugaban ta na jihar Katsina Kwamarad Mannir Suleiman a matsayin mamba na kwamitin kwararru na ƙasa

Bayanin haka na kunshe ne acikin wata sanarwa da sakataren kungiyar na ƙasa Auwalu Yusuf ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai.

Sanarwar dai na zuwa ne jim kaɗan bayan kammala taron Kungiyar karo na hamsin wanda ka gudanar a baban ɗakin taro, na kungiyar da ke Abuja.

Ƙungiyar tace ta ɗauki wannan shawara ne a bisa ƙwarewar sa da irin ayyuka da ya gudanar lokacin da ya ke riƙe da ƙungiyar a Jihar Katsina.

Sanarwar ta ce ta samu ammana da irin kwarewar Kwamarad Mannir Suleiman musamman wajen ciyar da kungiyar gaba a lokacin da yake shugabanci a matakin jiha.

Shima a nasa ta’aliki sabon shugaban kungiyar malaman kiwon lafiya, Kwamarad Bishir Ibrahim Gyaza ya bayyana tsohon shugaban kuma mamba a matakin ƙasa da cewa an dora ƙwarya a gurbin ta

“Wannan muƙami da Suleiman ya samu, ya dace ƙwarai duba da irin cigaba da ya samar lokacin da yake shugaban ƙungiyar a Katsina”.Gyaza yace.

Ya yi fatan zai amfani da ƙwarewar sa da jajircewar sa wajen ciyar da ƙungiyar a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya.

 

About The Author