Kungiyar Tuntuɓa Ta Dattawan Katsina Ba Ta Siyasa Ba ce. – Galadiman Katsina
Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi Mai Shari’a Sadiƙ Mahuta ya bayyana cewa kungiyar Tuntuɓa ta Dattawan Katsina bata da alaka ta nesa ko ta kusa da sha’anin siyasa.
Mai Shari’a yana magana ne a matsayin martani akan wani taron manema labarai da wasu mambobin kungiyar suka kira a satin da ya gabata inda suka bayyana cewa kungiyar ba zata zaɓi Bola Tinubu ba a shekarar 2027 idan ya sake tsayawa takara
An ruwaito sakataren kungiyar Tuntuɓa ta Dattawan Katsina Alhaji Sani Muhammad na yi wa shugaba Tunibu gargadi akan irin salon mulkin sa musamman saboda kama Ferfesa Yusuf Usman da aka yi wanda shima ɗan jihar Katsina ne.
Sai dai ga alamu waɗannan kalamai ba su yi wa sauran mambobin daɗi ba, musamman danganta kungiyar da sha’anin siyasa wanda suka ce ba a kafa kungiyar domin haka ba.
A cewar, Galadiman Katsina babu abinda ya haɗa kungiyar su da irin waɗannan kalamai, abinda suka sanya gaba shi ne, duk abinda zai taɓa wani ɗan jihar Katsina ko arewa to anan za a ga aikin su ba wata-wata ko jira.
“Misalin wannan magana shine kama Ferfesa Yusuf Usman da gwamnatin tarayya ta yi, mun yi kira cewa idan ya aikata laifi a gurfanar da shi gaban kotu idan kuma bai yi laifi ba, a sake shi, wannan shine matsayin mu” inji shi
Haka kuma lokacin da muka lura cewa aikin hanyar da ta taso daga Kano zuwa Katsina yana tafiyar hawainiya da kuma aikin titin jirgin kasa, sai da muka zauna da ministocin Buhari guda biyu Fashila Raji da kuma Rotimi Ameachi domin jin inda aka tsaya.
Sai dai ya cigaba da bayanin cewa, batun sake zaɓen Tinubu wannan maganar siyasa ce, ita kuma kungiyar Tuntuɓa ta Dattawan Katsina ba kungiyar siyasa ba ce, ya kamata al’umma su san haka.
Galadiman Katsina wanda yake mamba ne na wannan ƙungiya ya yi ƙarin haske da cewa, babu ruwan su ko wa za a zaɓa a shekarar 2027, batun zaɓe yana hannun al’umma ba kungiyar Tuntuɓa ta Dattawan Katsina ba.
Kazalika ya ƙara cewa suna nisanta kan su da irin waɗannan kalamai da Sakataren kungiyar Alhaji Sani Muhammad da ya yi a madadin su, saboda haka har yanzu matsayin kungiyar bai canza ba daga yadda aka san ta tun asali.
Idan za a iya tunawa a satin da ya gabata ne aka ruwaito Alhaji Sani Muhammad Yana bayanin cewa indai shugaba Tunibu zai cigaba da kame-kamen ‘yan arewa to kungiyar tana tabbatar masa da cewa ba za su sake zaɓen sa.
Waɗannan kalamai dai su ne suka tada hazo da Kura wanda har ta kai ga sauran mambobin irin sun Galadiman da sauran sun magantu tare da faɗin matsayin su game da waɗancan kalamai.
