September 18, 2026

Kungiyar Dikko Spotlight Ta Naɗa Manajan KTSTA Matsayin Uban Tafiyar Ta

0

Daga Babangida Sunusi, Kano

Aranar Alhamis ne kungiyar Dikko Spotlight takaima manajan hukumar zirga zirga tashar mota mallakatar gwamnati jihar Katsina Alhaji Haruna Musa Rugoji, karkashin jagoranci shugabanta Tsohon Dan takarar majalisa karamar hukumar Batsari Hon Manusr Garba Rumah.

Daya ke jawabi lokacin ziyarar shugaban kungiyar HON MANSUR GARBA RUMAH yace duba da irin gudunmuwar da shugaban hukumar yake badawa ga al’umma yabasu damar bashi uban tafiya wannan kungiya.

Rumah yakuma bayyana cewa zuwan Rugoji hukumar yasa hukumar tafarfado daga halin mutu kwai-kwai rai kwai-kwai data tsinci kanta,haka Kuma yana ganin shugowar manajan na KTSTA zai karama tafiyar wani ginshiki dazai taimaka wajen tafiyar.

Sannan yabayyana kungiyar datake fadakarwa kan jama’a suzabi dantakatar gwamnan jihar Katsina karkashin inuwar jam’iyyar APC a zabe Mai zuwa, Rugoji nada rawar takawa a wannan tafiya dan cigaban jihar Katsina ne gabansa.

Shima anasa jawabin Haruna Musa Rugoji yayi matukar godiya bisa wannan mukami da suka bashi,inda yayi alkawalin aiki tukuru dan samar da nasara a wannan tafiya.

Shugaban kungiyar dai yasamu rakiyar wasu daga cikin jigan-jigan kungiyar yayin ziyarar.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *