Ku Taimaka Ku Koma Karatu, Buhari ya Roki ASUU a Jawabinsa na Ranar Samun Ƴancin Kai
Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ya roki kungiyar malaman jami’o’in da ke yajin aiki da su koma azuzuwa.
Ya kuma ba su tabbacin cewa za a biya musu bukatunsu a cikin karancin lokaci.
A lokacin da yake jawabi ga al’ummar kasar a ranar Asabar don bikin murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai a Najeriya karo na 62, Manjo Janar mai ritaya ya bayyana bakin cikinsa kan yadda harkokin Ilimi ke tabarbarewa musamman manyan makarantu.
Ya ce, “Dole ne in furta cewa na ji takaicin yadda ake ci gaba da kawo cikas ga tsarin karatunmu na manyan makarantun gaba da sakandare, kuma ina amfani da wannan ranar ta bikin samun ‘yancin kai wajen sake jaddada kirana ga kungiyar malaman jami’o’in (ASUU) da ta dawo yajin aiki.
