Kisan Shiroro: Gwamnatin Neja Ta Dakatar Da Hako Ma’adanai A Kananan Hukumomi 3.
Biyo bayan harin da ‘yan bindiga suka kai a wani wurin hakar ma’adinai a unguwar Ajata Aboki da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja, gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello ya bayar da umarnin dakatar da duk wasu ayyukan hakar ma’adanai a kananan hukumomin Shiroro, Munya, da Rafi dake cikin jihar. Rohotonni dai sun ce an kashe mutane 48 a lokacin harin.
Sakataren gwamnatin jihar Ahmed Ibrahim Matane ne ya bayyana hakan jiya a Minna. Ya kuma ce dakatarwar ba ta da iyaka. Ya ce manufar kuma ita ce a magance yadda matsalar rashin tsaro ke ta karuwa a yankunan da lamarin ya shafa.
A cewar majiyar Popular News Hausa ta jaridar Leadership, gwamnatin ta ce wuraren hakar ma’adinan a yanzu suna tara mutane, har ma da masu laifi wadanda ke ma sha’anin tsaro barazana. Sakataren gwamnatin ya yi gargadin cewa duk mai hakar ma’adinan da aka kama yana hakar ma’adinai a yankunan zai fuskanci fushin doka.
