Kisan Ɗan Jarida: NUJ Ta yi Kira ga Jami’an Tsaro Su Gaggauta Gano Waɗanda Suka yi Kisan A Zamfara
Daga Hussaini Ibrahim
Kungiyar ‘yan jarida ta Kasa ta bayyana kisan gillar da aka yi wa wakilin gidan rediyon Muryar Najeriya Hamisu Danjibg a gidan da ke Gusau abin takaici ne kuma tayi kira ga jami’an tsaro da su gaggauta gano wanda suyi kisan domin a hukunta su.
Kungiyar ta yi kira ga hukumomin tsaro a jihar da su binciki lamarin tare da gurfanar da waɗanda suka aikata wannan aika-aika a gaban kuliya.
A sanarwa da ta fito ga sakataren kungiyar na jiha Ibrahim Ahmad Gada da yammacin Laraba a Gusau.
“Marigayi Hamisu Danjibga dan jarida ne wakilin Muryar Najeriya (VON) wanda aka tsinci gawarsa a cikin masai a bayan gidansa bayan kwana uku da batar shi”.
“An gano gawar tasa ne sakamakon wani wari mara dadi da yaran Islamiyya suk ji a yammacin ranar Laraba 20 ga Satumba, 2023 wanda ya ja hankalin malamansu.domin binciken Shadar”
Bayan da ya fasa masai ne aka tabbatar da gawar Danjibga da danginsa da wasu makwabta. tuni dai aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Kungiyar na mika ta’aziyya ga iyalai, da Muryar Nijeriya da ɗaukacin al’umma jihar Zamfara.
