September 18, 2026

Kisan Ɗan Jarida: ‘Yan Sanda A Zamfara Sun Kama Waɗanda Ake Zargi

0

Daga Hussaini Ibrahim

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta sanar da kama wasu mutane uku da ake zargi da kashe Marigayi Wakilin VON, Hamisu Danjibgan, Haruna Danjibga tare da waɗanda ake zargin sun sayi kadarori da aka kwashe bayan sun kashe Marigayin.

Waɗanda ake zargin a cewar rundunar ‘yan sandan, su ne Mansur Haruna wanda ya kasance dan uwan ​​marigayin ne da kuma abokin kinsa Ibrahim Nababa da kuma wanda ya sayi dukiyar marigayin da aka sace kuma dukkansu sun amsa laifin kashe Ɗanjibga.

Da yake gabatar da waɗanda ake zargin, kwamishinan ‘yan sanda, CP Mohammed Shehu Dalijan, ya ce da muka samu rahoton kashe ɗan jaridan ba tare da laifin kome ba, Hamisu Danjibga, ‘yan sanda sun ɗauki matakin cafke waɗanda ake zargin.

CP Dalijan, ya ce wanda ake zargin na farko, Mansur Haruna, wanda ya kasance Ƙanin Ɗan uwane ga marigayin, ya bayyanawa ‘yan sanda yadda suka yi ta fama da Ɗanjibga a lokacin da suke son sace shi, da kuma duk abin da ya faru da ya kai ga yanke hukuncin karshe na kashe shi. .

A wata hira da Mansur Haruna, ya bayyana cewa kawunsa, Danjibga ne ya kore shi daga gidansa saboda ya lura da yana sata, inda ya kara da cewa, “Kafin ya kore ni daga gidansa, sau biyu na tuntube shi ina neman ya tsaya mani na shiga aikin sojan da kuma ‘yan sanda, amma duk ya ki saboda mumunar dabi’a ta.

Rundunar ‘Yan Sandan su gabatar da takwaarorin su masu laifi daban daban da suka kama dan mika su koto da dan hukunta su.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *