Kirsimeti: Gwamna Inuwa Ya Taya Kiristoci Murna Ya Bukacesu Da Su Yi Addu’o’i Ga Jiha Da Kasa Kan Matsalolin Tattalin Arziki Da Tsaro
Daga Khalid Idris Doya
Yayin da Kiristocin Jihar Gombe ke bin sahun takwarorinsu na duniya wajen gudanar da bukukuwan Kirsimeti na bana, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bukaci masu bi su dabbaka dabi’un kauna, sadaukarwa da kuma hakuri kamar yadda kiyarwar Yesu Almasihu ta nunar.
A sakonsa na taya murna dauke da sanya hannun Ismaila Uba Misilli, babban daraktan yada Labarun gwamnan Jihar Gombe, Gwamna Inuwa Yahaya ya bukaci mabiya addinin na Kirista a Jihar Gombe dama daukacin al’ummar Nijeriya baki daya da su ci gaba da karfafa imaninsu da Allah, tare da tabbatar da zaman lafiya da hadin kai da kuma kyawawan dabi’un da za su kawo ci gaban jihar da kasa baki daya.
Ya kuma bukaci jama’a su sake sadaukar da kan su ga addu’o’i, abin da ya ce yana da matukar tasiri ga zaman lafiya da haɗin kan al’ummah.
Gwamnan ya bayyana cewa “A wannan muhimmin biki na Kirsimeti, ina mika sakon fatan alheri ga al’ummar Kirista da daukacin al’ummar kasar nan. Wannan lokacin yana tunatar da mu bukatar dabbaƙa kyawawan halaye na kauna, sadaukarwa da kuma hakuri. Ina kira a gare mu dukka, mu yi tunani a kan darussan wannan lokaci ke koyarwa da suka hada da kauna da soyayya da kuma kyauta”.
Da ya ke tabbatar da aniyar gwamnatin sa na ci gaba da bullo da tsare-tsare da manufofin da za su inganta hadin kai da zaman lafiya a jihar, Gwamnan ya bukaci jama’ar jihar su yi amfani da wannan lokacin wajen yiwa jihar da kasa addu’ar zaman lafiya da ci gaba don gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali.
“Ina kira a gare ku, ku yi amfani da wannan lokaci wajen sadaukar da kai cikin addu’o’i ga Allah Madaukakin Sarki don ya dawo mana da zaman lafiya a cikin al’ummar mu, mu yi addu’ar Allah Ya dawo mana da zaman lafiyan da aka dade ana mota, a yi mana addu’o’in zaman lafiya don samun zabe da mika mulki cikin kwanciyar hankali. Mu yi addu’a Allah ya sa Nijeriya ta fita daga cikin dimbin kalubalen da take fuskanta”.
Ya kuma bukaci al’ummar jihar kar su yanke kauna, amma su ci gaba da kasancewa da bege duk da irin kalubalen zamantakewa da tattalin arziki da duniya ke ciki, wadda cutar corona da yakin Rasha da Ukraine da kuma rashin tsaro da ake fama da shi a Najeriya suka haifar.
“Hakika muna cikin wani mawuyacin lokaci, amma ina da kwarin gwiwar cewa tare da sadaukar da kai, jajircewa da kuma komawa ga Allah ta hanyar addu’o’i da karfafa hadin kai, za mu shawo kan duk wadannan jarrabawa kuma mu yi nasara”.
